Maganar biyan basussukan da ma'aikatan Npower na wucin gadi nanan Daram a watan November kamar yadda Ministan tace.
Maganar biyan basussukan da ma'aikatan Npower na wucin gadi nanan Daram a watan November kamar yadda Ministan tace.
Idan baku manta ba Ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Dr Betta Edu, ta sanya watan fara biyan wasu makudan kudade na tsawon watanni 9 ga wadanda suka ci gajiyar Npower.
A cewar ministar a lokacin da take jawabi ga wadanda zasu ci gajiyar shirin Iyaloja market Monie a ranar Laraba daya daga bata ta baiyana Nasororin da ofishin ta ke samu karkashin shirin Renewed Hope.
Maganar biyan Renewed Hope Npower skills nanan daram kamar yadda tace cikin watan Nuwamba sannan za a bunkasa shirin cikin shekara mai zuwa
za a fara biyan wadanda suka ci gajiyar Npower kudaden alawus na tsawon watanni 9 cikin watan Nuwamba
Makwanni biyu da suka gabata ana ci gaba da biyan tallafin N25,000 na Conditional Cash Transfer Programme (Renewed Hope Conditional Cash Transfer Programme (RHCCT)’, inda miliyoyin zasu anfana
Ma’aikatar ta kaddamar da rijistar mata ‘yan kasuwa a kasuwanni 109 a fadin shiyyar majalisar dattawa ta tarayya, a cikin shirin bayar da lamuni na Iyaloja Monie, a cikin wannan Nuwamba, 2023.
Shirin Iyaloja Monie shiri ne na ba da lamuni, wani sabon salo na shirin GEEP Loan Programme, wanda ta hanyar da masu cin gajiyar shirin, mata ‘yan kasuwa, za su karbi lamuni marar ruwa na N50,000 kowanne.
A cewar Ministan Dr Better Edu, shirin bayar da lamuni na Iyaloja Monie an yi niyya ne ga masu cin gajiyar Miliyan 1.5 a fadin Jihohi 36
Shirin bayar da rancen zai kasance na samar da ‘yan kasuwa masu fama da talauci, da taimaka musu wajen inganta jarinsu da fadada sana’o’insu, a wani bangare na kawar da ‘yan Nijeriya daga talauci mai dimbin yawa da kuma matsalolin jin kai.
Za a aiwatar da Shirin Lamuni na Iyaloja Monie a matakai 3 tare da masu cin gajiyar 500,000.
Credit /Shamsu Yarima
0 Response to "Maganar biyan basussukan da ma'aikatan Npower na wucin gadi nanan Daram a watan November kamar yadda Ministan tace. "
Post a Comment