JIHAR JIGAWA TA CIKA SHEKARU 32
Sunday, 27 August 2023
Comment
JIHAR JIGAWA TA CIKA SHEKARU 32
A yau Lahadi, 27 ga Augustar 2023, Jiharmu ta Jigawa take cika shekaru 32 da samuwa. Muna taya juna murna da Allah Ya bamu tsawon rai da lafiyar ganin wannan lokaci. Muna fatan Allah zai sake ara mana kwanakin ganin ɗorewar Jiharmu zuwa shekaru masu yawa.
Babu shakka, mun ɗauko tafiya mai nisa a tsawon waɗannan shekaru kuma Jigawa ta samu nasarori da dama. Amma akwai sauran tafiya a gaba domin har yanzu bamu kai inda muke burin kaiwa ba. An barmu a baya ta fannoni daban-daban, ciki har da jihohin da aka ƙirƙira tare damu, wasu ma a bayanmu.
Allah Ya bamu ikon haɗa kai da jajircewa domin yin aikin da zai mayar da Jiharmu abin misali a Najeriya da duniya bakiɗaya.
CREDIT :Santurakin Dutse
0 Response to "JIHAR JIGAWA TA CIKA SHEKARU 32"
Post a Comment