TOFA RAAYIN NASIRU SALISU ZANGO AKAN JANYE TALLAFIN MAI
A Fahimta ta…
Ni Ba masanin tattalin arziki bane amma dai Ina daga cikin masu ji a jikin su Dan haka na tabbatar ido ba mudu ba yasan kima.
Babban aikin dake gaban gwamnati shine samar wa jama‘ar ta sauki da tausaya musu lokacin da lamari ya cakude musu.
Amma Mu a Nigeria, An janye tallafi wanda aka yi tayi mana karyar cewar ‚yan kalilan ne ke morar sa,a dalilin janyewar farashin kayan abinci yayi bala‘in tsada, lokaci guda an sake janye tallafin Dala Nan ma abubuwa sun kara tsefewa, an janye tallafin jami‘oi nan ma kudin makaranta ya ninka sau uku.
Duk wadannan bala‘oi da ake an tayo mana babu wani abu guda daya tak da aka tanada domin rage mana radadi Dan Allah wannan wane irin tsari ne?
Ya kamata a ringa barin Mu Muna sosa dukan kafin a kara mana wani. Mun zama masu jiran tsammani kullum muka wayi gari saurare muke muji wacce sabuwar masifar za‘a jefo?
Allah kasa ya zame mana kaffara, Allah yasa wannan dukan yasa Mu shiga hankalin mu lokacin zabe mu bude ido mu yiwa kan mu adalci mu zabo wanda muke wa zaton zai kamanta tausayi, Allah ya bamu ikon zabe bisa cancanta Ba bisa son rai ko kishin jam‘iyya ba.
0 Response to "TOFA RAAYIN NASIRU SALISU ZANGO AKAN JANYE TALLAFIN MAI "
Post a Comment