--
Tofa :Dalilin da ya sa ban yi Tinubu a zaɓen fidda-gwani ba - Abdullahi Adamu

Tofa :Dalilin da ya sa ban yi Tinubu a zaɓen fidda-gwani ba - Abdullahi Adamu

>


 Dalilin da ya sa ban yi Tinubu a zaɓen fidda-gwani ba - Abdullahi Adamu 

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya bayyana dalilin da ya sa ya nuna goyon bayansa ga tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan a yayin babban taron jam’iyyar a watan Yunin 2022.


Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa a yayin yaƙin neman zaben-fidda gwani na jam’iyyar APC, Adamu ya bayyana Lawan a matsayin dan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar.


Sai dai nan take shugaban ya fitar da wata sanarwa, inda ya nisanta kansa da wannan amincewa da aka ce an yi.


Da ya ke magana yayin wata tattaunawa da Arise TV a jiya Laraba, Adamu ya yi ikirarin cewa zabin Lawan shi ne matakin da kwamitin ƙoli na jam’iyyar, NWC ya yanke.

Ya ce: “Gaskiya ne, kuma ba zan musanta hakan ba, kuma ban musanta gaskiyar lamarin ba a lokacin da na gabatar da jawabin ga kwamitin ƙoli na kasa, sunan shugaban majalisar dattawa a lokacin, Ahmad Lawan, shi ne aka bayar a takarar shugabancin kasa.

“Hakan ya kasance kafin taron. Abubuwa da yawa sun faru tsakanin lokacin da ainihin ranar taron. 

“Kwana ɗaya bayan taron, mun je gidansa (Tinubu). Na kai na jagoranci daukacin kwamitinm na kasa zuwa gidansa da ke Asokoro, a nan Abuja, na kuma ba shi [Tinubu] goyon bayanmu. Muka tabbatar masa.

CREDIT. Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "Tofa :Dalilin da ya sa ban yi Tinubu a zaɓen fidda-gwani ba - Abdullahi Adamu "

Post a Comment