Duba muhimman abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da farfaɗiya.
Farfaɗiya | Me Ke Faruwa A Ƙwaƙwalwar Ne?
Duba muhimman abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da farfaɗiya.
1. Kimanin mutum miliyan 50 ke fama da farfaɗiya a faɗin duniya, hakan ya sanya ta cikin lalurorin ƙwaƙwalwa mafi shahara a duniya.
2. Kusan kaso 80 cikin 100 na masu farfaɗiya suna zaune ne a ƙasashe masu ƙaranci da matsakaicin tattalin arziƙi.
3. An yi kiyasin cewa har kaso 70 cikin 100 na masu farfaɗiya na iya rayuwa ba tare da bugun farfaɗiyar ba idan aka gano lalurar da wuri kuma ake karɓar maganin da ya kamata.
4. Saboda haɗuran da suke fuskanta a rayuwa, masu farfaɗiya na da ninki uku na haɗarin mutuwa da ƙuruciya fiye da sauran mutane.
5. Kaso uku cikin huɗu na masu farfaɗiya da ke zaune a ƙasashe masu ƙarancin tattalin arziƙi ba sa iya samun magani da kulawar da suka kamata.
6. A sassan duniya da yawa, masu farfaɗiya da iyalansu na fuskantar tsangwama da wariya.
7. Farfaɗiya lalurar ƙwaƙwalwa ce da wani ba ya iya harbin wani ko shafa wa wani. Haka nan, tana iya samun kowa kuma a kowane zangon shekaru na rayuwa.
8. Farfaɗiya na iya zama daga sabuba kamar haka:
i. Lahanin ƙwaƙwalwa ga jariri kafin ko yayin haihuwa.
ii. Tawayar halittar ƙwaƙwalwa ko laka.
iii. Lahani ko bugu a kai.
iv. Shanyewar ɓarin jiki.
v. Harbin ƙwayar cuta ga ƙwaƙwalwa, kamar sanƙarau.
vi. Kansa / dajin ƙwaƙwalwa, da dai sauransu. Sai dai, duk da haka, kaso 50 cikin 100 na masu farfaɗiya ba a san haƙiƙanin sababin farfaɗiyar ta su ba.
9. Farfaɗiya na zuwa da bugun farfaɗiya wanda ke bayyanar da jijjiga a sashin jiki ko kuma dukan jikin. Bugun farfaɗiya sau da yawa na zuwa da fitar hayyaci ko gushewar hankali na wani ɗan lokaci. A wasu lokutan tare da sakin fitsari ko fitar bayan gida.
10. Saboda ƙwaƙwalwa, laka da jijiyoyin laka suna aiki ne da tsarin lantarki, farfaɗiya lalura ce sakamakon rikicewar tsarin lantarkin ƙwaƙwalwa a wani sashi ko sassan ƙwaƙwalwa. Don haka, ba bugun aljani ba ce!
Shiga Whatapp group din mu kasamu wasu labaran 👇
https://chat.whatsapp.com/IIravnNrHUhEoRofjyuTtN
CREDIT. PHYSIOTHERAPY HAUSA.
0 Response to "Duba muhimman abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da farfaɗiya."
Post a Comment