Ɗan kasuwa Eze ya baiwa Jami'ar Azman gudunmawar Naira miliyan 200 a Kano
Ɗan kasuwa Eze ya baiwa Jami'ar Azman gudunmawar Naira miliyan 200 a Kano
Wani hamshakin attajirin dan kasuwa, Arthur Eze, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 200 domin bunkasa jami’ar Azman ta Kano.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, Eze, wanda shi ne aka naɗa a matsayin uba ga sabuwar jami’ar, ya yi magana a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin amintattu da majalisar gudanarwar jami’ar a Kano ranar Lahadi.
Ya kuma yaba wa wanda ya kafa jami'ar tare da yin alkawarin ci gaba da tallafawa manufofin ta domin samun ci gaban da ake buƙata.
Eze ya tuna yadda ya samu kyakykyawar alaka a Arewacin Nijeriya, musamman a Kano, a zamanin marigayi tsohon gwamnan Kano Abubakar Rimi, lokacin da aka riƙa ba shi kyautar gurbi a gidan Talabijin na gwamnati daya tilo a lokacin wato CTV Kano.
A nashi ɓangaren, shugaban kwamitin gudanarwar jami’ar, AbdulManaf Sarina, ya ce nadin Eze a matsayin shugaban jami’ar ya zo ne saboda irin gagarumin ci gaban da ya samu wajen bunkasa ilimi a fadin Nijeriya.
Sarina, wanda shi ne wanda ya kafa jami’ar kuma shugaban jami’ar, ya yi alkawarin tabbatar da inganci a matsayin tubalin gina jami'ar.
CREDIT. Daily Nigerian Hausa.
0 Response to "Ɗan kasuwa Eze ya baiwa Jami'ar Azman gudunmawar Naira miliyan 200 a Kano "
Post a Comment