Dalilin cutar Bashir /illarsa da kuma maganin sa
Aisha health talk
Kalmar "Basur" a Turance cutar na da sunaye da dan dama (Haemorrhoids, Piles & Hemorrhoidal disease) wata cuta ce da jijiyoyin ta-kashin mutum wanda ke dauke da jini kan kumbura daga ciki, galibi jijiya daya ce ko biyu, wani sa'i kuma ta waje ne, sai ya zama kamar wani tsiro, sau tari ba ma a sanin ainihin dalilin kamuwa da cutar, sai dai daskarewar kashi a ciki da mutum yakan yi ta turo shi da qarfi kan matsa wa wurin, yakan faru ga mace mai juna biyu, cikin yakan matsa wa jijiyoyin butiyar. (NAU'IKAN BASIR
Akwai cutar basir ta cikin ciki, ita ce cutar da jijiyoyin jini dake cikin ta kashi suke kumbura, wani sa'in jini kan fito ba tare da jin wani radadi ba, in abin ya ci gaba kuma sai jijiyoyin su kwanto cikin ta-kashin a yayin fitar ba-haya, wannan nau'in ya rabu har zuwa matakai 4:a) Matakin farko: Jijiyoyin kan kumbura a cikin takashin amma ba ya fitowa waje.
b) Na buyu: Sukan kumbura kuma su leqo waje wani sa'in yayin ba-haya ko fitar tusa, sai dai in aka kammala yakan koma ciki. .
c) Na uku: Jijiyoyin da kansu sukan leqo waje batare da fitar ba-haya ko wani abu ba, ba su cika komawa ba sai in majinyacin ne ya mayar da su
d) Wannan in jijiyoyin suka leqo waje shi kenan, ko an mayar da su ba sa komawa, dan kanoma na zahiri kenan.
2) Basur dai dake waje:hi
wannan jijiyar da suka kumburan asali ba a ciki suke ba, a waje suke, majinyaci bai jin wani radadi in ba an sami daskarewa ne a jijiyoyin da jini ke bi ba, kuma ba a ganin jini sai in jijiyar da ta kumbura ne ta fashe.
DALILIN KAMUWA DA CUTAR
Duk da cewa manya-manyan dalilan dake kawo basir ba fayyatattu ba ne sai dai akwai wasu abubuwa da ake zaton tabbas za su iya haifar da cutar:
1) Meqewar bayan mutum sambal ba tare da ta dan shiga ciki ba, wannan yakan taimakawa wajen tunkudan jinin dake zuwa ta-kashi, masu wannan tunanin suke ganin shi ya sa dabbobin dake tafiya da qafa 4 ba sa basir. 2
CREDIT 👉Aisha health talk
0 Response to "Dalilin cutar Bashir /illarsa da kuma maganin sa "
Post a Comment