--
DADUMINSA :Emefiele Ya Lalata Tsarin Kudin Najeriya - Tinubu

DADUMINSA :Emefiele Ya Lalata Tsarin Kudin Najeriya - Tinubu

>

 



Emefiele Ya Lalata Tsarin Kudin Najeriya - Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana sabon matsaya dangane da dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele. 

Tinubu ya yi magana a yayin tattaunawa da yan Najeriya mazauna kasar Faransa da kasashen da Turai da ke makwabtaka a gefen taron Duniya a babban birnin kasar Faransa, Paris a ranar Juma'a.

Shugaban ya ce tsarin kudin kasar a karkashin dakataccen gwamnan na CBN ya lalace. 

Tinubu ya bayyana abun da ya kai ga shigarsa halin da yake ciki ya ce yan Najeriya da dama mazauna waje sun gaza tura kudi ga yan uwansu saboda farashin chanjin kudi, cewa wannan ya zama tarihi a yanzu. 

Yace "Lokacin tsarin kudi ya lalace. Yan mutane kadan ke kunshe kudadenmu a jakunkuna sannan kuma ku da kanku, kun daina tura kudi gida ga iyayenmu talakawa. 

Kafofi da dama...amma wannan ya zama tarihi a yanzu, ya zama tarihi. 

"Mutumin na a hannun hukumomi, ana yin wani abu a kai. 

A farkon wannan watan ne dai shugaba Tinubu ya dakatar da Emefiele daga kan muƙamin na sa, kuma tuni hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta yi awon gaba da shi

Shiga Whatapp group din mu kasamu wasu labaran. 

https://chat.whatsapp.com/GMq7XVb0Eyj8UgOVB1HGlN

CREDIT. Liberty Radio Kano. 

0 Response to "DADUMINSA :Emefiele Ya Lalata Tsarin Kudin Najeriya - Tinubu"

Post a Comment