--
YANZU-YANZU :Muƙabala: Young Sheikh ya buƙaci Gwamnan Bauchi da ya barshi da Dr. Idris su yi zama.

YANZU-YANZU :Muƙabala: Young Sheikh ya buƙaci Gwamnan Bauchi da ya barshi da Dr. Idris su yi zama.

>



Muƙabala: Young Sheikh ya buƙaci Gwamnan Bauchi da ya barshi da Dr. Idris su yi zama. 


“Matashin Malamin nan na Addinin Musulunci wanda ya Shahara a Fannin Ilmuma daban-daban wato Zakir M.S. Ali Young Sheikh Zariya, Ya Bayyana Cewa; Shine ya fi kamata da ya zauna da Dr. idris Abdulaziz Bauchi saboda sauran malaman sunyi girma akan zama dashi su tattauna mas'alar bayanan taimakon manzon Allah (SAW) idan Musulmi zai yi tawassil da ma'aiki, saɓanin yadda shi Malamin yake ikirarin Musulmi bai kamata ya yi Tawassil da Annabi ba, idan ya ta shi neman wani abu daga wurin Allah (SWA), Matsayar ba Allah ba, har shi malamin yake cewa; ba ya bukatar taimakon Annabi (SAW).


“Dr. Idris Abdul'aziz dai Fitaccen Malamin Addinin Musulunci ne ɗan Asalin jihar Bauchi, ganin yadda kalaman malamanin ya tada ƙura a Najeriya baki daya.” 


“Zakir Young Sheikh, ya yi Kira da Babban murya ga gwamnatin jihar Bauchi kan cewa; a hutar da malaman da zasu zauna da shi malamin shi kadai kawai ya ishe shi gayya, zai iya tasowa daga birnin Zariya Jihar Kaduna zuwa Bauchi matsayar an yarje masa da wannan buƙatan nasa ta gaggawa.”


Bugu da kari Young. Sheikh ya ce ya tanaji ruwan hujjoji domin kafawa Dr. Idris ɗin a cikin Al-Qur'ani Mai Girma.


Idan dai Allah ya kai mu gobe Asabar ne dai za'ayi wanna zaman da shi Dr. Idris din da wasu malaman Addinin Musulunci, wanda Gwamantin Jihar Bauhci ta ɗauki nauyin wannan Muƙabalan”


CREDIT 👉Jaridar Alfarma. 

0 Response to "YANZU-YANZU :Muƙabala: Young Sheikh ya buƙaci Gwamnan Bauchi da ya barshi da Dr. Idris su yi zama. "

Post a Comment