--
YANZU-YANZU :Bola Ahmed Tinubu baya saudiyya Ana zargin yana asibiti

YANZU-YANZU :Bola Ahmed Tinubu baya saudiyya Ana zargin yana asibiti

>



Tinubu Baya Makkah Kamar Yadda Abokan Aikinsa Suka Fada; APC Na Boye Yanayin Lafiyarsa, da Inda Yake – Sowore


Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya ce " zababben shugaban kasa ", Bola Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki, bai je Makkah, Saudi Arabia ba, a lokacin bukukuwan azumin Ramadan, kamar yadda masu kula da shi suka ce.


Masu kula da tinubu sun yi ikirarin cewa tsohon gwamnan jihar Legas da ke fama da rashin lafiya wanda ya je birnin Paris na kasar Faransa jim kadan bayan kammala zaben ranar 18 ga watan Maris, ya je Makka ne domin gudanar da bukin azumin Ramadan.


An kuma lullube hakikanin yanayin lafiyar tinubu yayin da jam’iyyarsa ta APC, ta dage cewa ya tafi kasar waje domin hutawa bayan ya yi yakin neman zabe.


Amma Sowore a ranar Asabar ya ce masu rike da Tinubu sun yi karya game da zuwansa Makka, inda suka ce Tinubu baya tare da Buhari kuma ba a ganinsa a ko’ina a Makka


CREDIT 👉👉DailyTrueHausa

0 Response to "YANZU-YANZU :Bola Ahmed Tinubu baya saudiyya Ana zargin yana asibiti"

Post a Comment