YANZU-YANZU :Zan Gina Katafaren Makarantar Haddar Kur'ani Da Sunan Sheik Dahiru Bauchi, Cewar Gwamna Bala
Sunday, 12 March 2023
Comment
Zan Gina Katafaren Makarantar Haddar Kur'ani Da Sunan Sheik Dahiru Bauchi, Cewar Gwamna Bala
Za a gina babban katafaren cibiyar haddar Alkur'ani mai girma ta zamani a jihar Bauchi mai suna "Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA" wanda mai girma gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Ƙauran Bauchi ta dauki nauyin ginawa.
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Mohammed ya fadi hakan ne, a yayin da ya kai ziyara girmamawa ga babban Malamin a gidan sa dake titin Bauchi zuwa Gombe, inda ya tabbatar da fara aikin cikin kankanin lokaci da yardar Allah.
CREDIT 👉👉Rariya
0 Response to "YANZU-YANZU :Zan Gina Katafaren Makarantar Haddar Kur'ani Da Sunan Sheik Dahiru Bauchi, Cewar Gwamna Bala "
Post a Comment