YANZU-YANZU :Shawarar dakatar da gine-gine: Ganduje ya maida wa Abba Gida-Gida martani
Shawarar dakatar da gine-gine: Ganduje ya maida wa Abba Gida-Gida martani
Gwamnatin Kano ta yi kira ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi haƙuri, ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara ga jama'a.
A cewarta, irin wannan shawara za ta iya haddasa ruɗani na babu gaira babu dalili a cikin jihar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba ya fitar don maida martani ga ofishin zaɓaɓɓen gwamnan a kan su guji janye daga filayen gwamnati.
Gwamnatin Kano ta ce abin da zaɓaɓɓen gwamnan ya yi na bayar da umarni a kan wani batu da ya shafi manufar gwamnati, daidai lokaicn da gwamna mai c har yanzu yake kan muli, tamkar riga mallam masallaci ne.
Ta ƙara da cewa kamar yadda yake ƙunshe a cikin tsarin mulkin Najeriya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai ci gaba dazama gwamna mai cikakken iko har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, kuma yana da damar gudanar da ayyukansa hatta a ranar jajiberen saukarsa daga mulki.
A jiya ne, gwamnan mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf ya fitar da wata sanarwa wadda ya bayyana a matsayin shawara, yana kira ga masu gine-gine a filaye da wuraren gwamnati, ciki har da masallatai da maƙabartu da makarantu da sauransu, su dakata.
CREDIT 👉👉Daily Nigerian Hausa via Facebook.
0 Response to "YANZU-YANZU :Shawarar dakatar da gine-gine: Ganduje ya maida wa Abba Gida-Gida martani "
Post a Comment