--
YANZU-YANZU :Ƴandaba sun farfasa sakateriyar hukumar yaƙi da dabanci a Zamfara

YANZU-YANZU :Ƴandaba sun farfasa sakateriyar hukumar yaƙi da dabanci a Zamfara

>





Ƴandaba sun farfasa sakateriyar hukumar yaƙi da dabanci a Zamfara 


Wasu ƴandaba sun lalata sakatariyar hukumar yaki da dabanci ta Zamfara a rikicin da ya barke a jihar a ranar 21 ga watan Maris bayan sanar da sakamakon zaben gwamna a jihar.


Kwamandan rundunar, Bello Bakyasuwa ne ya bayyana haka yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Gusau a ranar Asabar.


Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, a ranar 21 ga watan Maris, an samu rikice-rikice a Gusau, babban birnin jihar, bayan da wasu batagari suka saje da magoya bayan jam’iyyar PDP domin murnar nasarar zaben gwamna.


Rikicin ya kai ga lalata ofisoshin jam’iyyar APC, allunan talla, lalata da kuma wawure ofisoshin gwamnati da kadarori na miliyoyin naira.


Rundunar ‘yan sandan jihar a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce ta kama wasu mutane 40 da ake zargin ƴandaba ne da laifin tashin hankalin.


 Bakyasuwa ya bayyana tashin hankalin a matsayin wani mummunan lamari.


Ya yi Alla-wadai da matakin sata da lalata kaya da wasu da ake zargin magoya bayan jam’iyyar PDP su ka yi a jihar.


Ya yi nuni da cewa hukumar ba ta ɗauki ɓangarancin siyasa ba kuma Gwamna Bello Matawalle ne ya kafa ta ne domin ta taimaka wa hukumomin tsaro, domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.


A cewarsa, ƴandaban sun kuma sace motocin hukumar guda biyu da suka hada da kirar Hilux da saloon kirar Peugeot 406 mallakar hukumar.


Ya ce barayin sun sace kadarori da kudinsu ya kai Naira miliyan 50 a Sakatariyar.

CREDIT 👉Daily Nigerian Hausa. 

0 Response to "YANZU-YANZU :Ƴandaba sun farfasa sakateriyar hukumar yaƙi da dabanci a Zamfara "

Post a Comment