--
TOFA:Ƴan jam'iyyar NNPP na zanga-zanga kan ma'aikacin INEC da lokacin ritayar sa ya yi amma ya ƙi tafiya a Kano

TOFA:Ƴan jam'iyyar NNPP na zanga-zanga kan ma'aikacin INEC da lokacin ritayar sa ya yi amma ya ƙi tafiya a Kano

>

 




YANZU-YANZU: Ƴan jam'iyyar NNPP na zanga-zanga kan ma'aikacin INEC da lokacin ritayar sa ya yi amma ya ƙi tafiya a Kano


Magoya bayan babbar jam'iyyar adawa ta NNPP sun yi tsinke a kofar shelkwatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta, INEC,  a jihar Kano don neman wani babban ma'aikacin hukumar, Garba Lawan da ya yi ritaya.


Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tun tuni lokacin hutun wata uku na kafin ritaya ya yi amma Garba Lawan, wanda shi ne Babban Sakataren hukumar a reshen Kano, ya ƙi tafiya.


Yan NNPP Kwankwasiyya na zargin dai Garba Lawan ya ƙi tafiya hutun ne bisa haɗin baki da jam'iyyar APC don shirya maguɗin zaɓe a zaɓen gwamna mai zuwa ranar Asabar, kamar yadda a ka yi a 2019.


Ƙarin bayani na nan tafe...


CREDIT Daily Nigerian Hausa via Facebook search.

0 Response to "TOFA:Ƴan jam'iyyar NNPP na zanga-zanga kan ma'aikacin INEC da lokacin ritayar sa ya yi amma ya ƙi tafiya a Kano"

Post a Comment