--
TOFA YANZU-YANZU :Ƴan adawa na shirin daƙile rantsar da Ni a matsayin shugaban ƙasa, rantsuwata, in ji Tinubu

TOFA YANZU-YANZU :Ƴan adawa na shirin daƙile rantsar da Ni a matsayin shugaban ƙasa, rantsuwata, in ji Tinubu

>






Ƴan adawa na shirin daƙile rantsar da Ni a matsayin shugaban ƙasa, rantsuwata, in ji Tinubu 


Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya zargi wani shiri da wasu ƴan siyasa ke kullawa don dakile shirin mika mulki, musamman da ake sa ran rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.


Tinubu a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun daraktan hulda da jama’a na yaƙin zaɓen sa, kuma karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo SAN ya kuma gargadi ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da na Labour Party LP, Mista Peter Obi kan daukar matakin yin zanga-zanga, yayin da kuma su ke ci gaba da shari'arsu a gaban kotu.


A cikin sanarwar da aka fitar a yau Asabar a Abuja, zababben shugaban kasar ya bayyana cewa wadanda suka fito kan tituna suna zanga-zangar nuna rashin amincewa da zaɓen sa, na yin hakan ne don a kafa gwamnatin riko a ƙasar.


Wani bangare na sanarwar yana cewa; “Mun lura da matukar damuwa game da ayyukan da wasu mutane da kungiyoyi ke yi masu son murkushe dimokuradiyyar mu.


“Saboda dalilan da su suka san su, wadannan mutane sun ci gaba da kokawa kan yadda aka ayyana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben 2023. Sau tari, amma abin takaici, wadannan bata gari sun yi ta kiraye-kirayen a soke zaben ko kuma kada a rantsar da zababben shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu, 2023.


“Muna so mu nanata kuma mu jaddada cewa wannan mataki nasu bai dace da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin mu ko kuma dokokin zaben mu ba. Da mun dauki wadannan a matsayin son rai, duk da haka, saboda tasirinsu ga tsaron kasa da zaman lafiyar jama’a, don haka muka ga ya zama dole, idan ba haka ba, mu taka musu birki.

CREDIT 👉👉Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "TOFA YANZU-YANZU :Ƴan adawa na shirin daƙile rantsar da Ni a matsayin shugaban ƙasa, rantsuwata, in ji Tinubu "

Post a Comment