--
MATA KU FAHIMCE NAMIJI

MATA KU FAHIMCE NAMIJI

>





MATA KU FAHIMCE NAMIJI


1.A lokacin da kuke soyayyah da shi akwai son fahimtar junan ku,wanda wannan fahimtar ce zata saka har zuwa ga cikar muradin ku,kun auri junan ku,a lokacin tarayyar ku zaku iya sanin wasu daga cikin halayyan junan ku,wanda zaku iya son zaman ku a tare da junan ku,amma dole ne mace sai tafi yiwa Namiji uziri.


2.wata kullum zata ce akallah sai sunyi waya sau uku ko sama da hakan, idan basuyi ba kuma baya son ta,wannan ba gaskiya bane saboda Namiji wani dan kasuwa ne,wani Kuma ma'aikaci ne,wani ayyuka na masa yawa sosai ta yadda dole ne sai kin masa uziri bawai rashin so bane,wani baya samun kansa da wuri har sai dare,a lokacin yake da lokacin kan sa,to irin hakan sai ana yiwa juna uziri ki fahimce sa ya fahimce ki.


3.Akwai wanda zaki ga yana cika ki da son surutu da waya,da wasu kalamai amma kuma bake yake so ba, saboda yawan kiran waya bashi bane soyayyah kowa da yadda ya dauki soyayyah,idan kin gane zaki tsira kowa da yadda yake tsarin rayuwar sa.


4.hakuri da juriya a lokacin don dole ne sai ana yin hakuri da junan ku,akwai sab'ani tsakanin masoya wani lokacin aga kamar an rabu sai kuma a kara dawowa.


5.Idan kuka fahimci halin junan ku sai abin yazo maku da sauki,wani namijin ne mai saurin fushi,wata kuma macen ce mai saurin fushi da zuciya.

Duk lokacin da daya ya gane matsalar dayan to sai yasan yadda zai yi hakurin zama dashi.


©️ Nusaiba Tasiu Abdulrahim


CREDIT 👉👉sirrin rike miji on Facebook search 

0 Response to "MATA KU FAHIMCE NAMIJI"

Post a Comment