YANZU-YANZU: IPMAN ta umarci mambobinta da su rufe gidajen mai
Tuesday, 7 February 2023
Comment
YANZU-YANZU: IPMAN ta umarci mambobinta da su rufe gidajen mai
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta ƙasa, IPMAN, ta umarci mambobinta da su dakatar da duk wasu ayyuka a fadin kasar.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar ta IPMAN, Mohammed Kuluwu ya sanyawa hannu a yau Talata, an kuma umarci ‘yan kasuwar da su dakatar da biyan kudaden dakon man fetur da su ka fito daga tushe har sai an sanar da su.
Kungiyar ta ce shawarar ta biyo bayan "matsanancin halin da ake ciki yayin da ya ke shafar yadda mu ke samar da man da siyar da cikin asara (sic) da kuma matakin da hukumar ta dauka na tursasa su sayar da man a kan sabon farashi wanda hakan ya sa su ke samun faduwa,".
Source, Daily Nigerian Hausa via Facebook search.
0 Response to "YANZU-YANZU: IPMAN ta umarci mambobinta da su rufe gidajen mai"
Post a Comment