Kwankwaso ne Aminu Kanon wannan zamanin ~ Dan Sarauniya
Kwankwaso ne Aminu Kanon wannan zamanin ~ Dan Sarauniya
Tsohon kwamishinan ma'aikatar ayyuka na jihar Kano, Injiniya Muaz Magaji (Dan Sarauniya) ya sallamawa tsohon gwamnan Kano, kuma dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a batun siyasa a jihar Kano, inda ya bayyana shi a matsayin Aminu Kano na wannan zamanin.
Tarihi ya nuna cewa, Aminu Kano ya goyi bayan Marigayi Abubakar Rimi har ya zama gwamnan Kano a jam'iyyarsa ta PRP, amma sai sabani ya shiga tsakani bayan an kafa gwamnati, har Rimi ya fice daga jam'iyya, Marigayi Aminu Kano ya tsayar da Sabo Bakin Zuwo a zaɓe na gaba, kuma suka kayar da Rimi aka kafa sabuwar gwamnati.
Siyasar Kano dai salon ta daban ne, domin ko zaɓen shekarar 2019, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya sha dakyar ne a hannun tsohon mai gidansa Kwankwaso, ta hanyar zaɓen Inkwankulusib wanda ya bashi damar sake zama gwamna a karo na biyu.
Tuni masana suka yi kiyasin cewa, siyasar Kano a wannan zamanin tana hannun Kwankwaso, domin a kalla kaso 70% na masu goyon bayan yan siyasa a mutanen jihar suna tare dashi.
Daga: Kano Online News
26/2/2023
CREDIT /Daily Trust Hausa via Facebook search.
0 Response to "Kwankwaso ne Aminu Kanon wannan zamanin ~ Dan Sarauniya"
Post a Comment