--
 DADUMINSA :Zaɓen sanatoci: Kawu Sumaila ya yi zargin ƙona cibiyar tattara sakamako a Kano-ta-Kudu

DADUMINSA :Zaɓen sanatoci: Kawu Sumaila ya yi zargin ƙona cibiyar tattara sakamako a Kano-ta-Kudu

>

 




Zaɓen sanatoci: Kawu Sumaila ya yi zargin ƙona cibiyar tattara sakamako a Kano-ta-Kudu


Dan takarar kujerar majalisar dattawa na jamiyyar NNPP a yankin Kano-ta-Kudu, Suleman Abdurrahman Kawu Sumaila ya 

 bukaci jami'an tsaro, hukumar zabe mai zaman kanta, INEC da masu sanya idanu na ciki da wajen Najeriya da su kai ɗauki yankin.


Kawu Sumaila, ya bayyana haka ne lokacin da yake yiwa manema labarai karin bayani a Kano a yau Lahadi kan batun kona cibiyar tattara sakamakon zabe da aka yi a karamar hukumar Takai dake yankin.


A cewar sa, harin ya yi sanadiyyar rasa ran mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama. 


Tsohon dan majalisar wakilan ya kuma yi zargin cewa bayanan sirri da su ka samu ya nuna cewa Sanata Kabiru Gaya ne ya hada ƴan daban su ka kai harin.


Ya kuma kara yin zargin cewa yanzu haka Sanata Gayan na ƙara kitsa kai hari a ɗaya cibiyar tattara sakamakon zaɓe da ke Rano.


Don haka ya yi kira ga jami'an tsaro da su tura tawagar gaggawa zuwa wannan yanki domin kare aukuwar haka a gaba, inda yace helkwatar tattara sakamako dake karamar hukumar Rano wadda ita ce ke karbar sakamakon mazabar baki daya, ita ce ya kamata a tsaurara matakai a cikin ta.


Da yake tabbatar da harin, mai magana da yawun rundunar yan sanda ta Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya ce cikin gaggawa aka kwashe baki dayan kayayyakin zaben, kana kawo yanzu an kama mutane 3 da ake zargi da hannu a harin.


Ya kuma tabbatar da cewa tuni zaman lafiya ya dawo a yankin, inda a cewar sa, har an kawo sakamakon nantakai zuwa matattarar sakamako ta yankin.


SP Kiyawa ya kuma ce an kara kai jami'an tsaro domin karfafa tsaro a yankin.


Source /credit /Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to " DADUMINSA :Zaɓen sanatoci: Kawu Sumaila ya yi zargin ƙona cibiyar tattara sakamako a Kano-ta-Kudu"

Post a Comment