DADUMINSA, Kwankwaso ya doke Tinubu a mahaifar Ganduje
Sunday, 26 February 2023
Comment
Kwankwaso ya doke Tinubu a mahaifar Ganduje
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, NNPP, Rabi'u Kwankwaso ya yi nasara a karamar hukumar Dawakin-Tofa, mahaifar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
Kwankwaso ya doke Bola Tinubu, daya daga cikin manyan abokan hamayyarsa na jam’iyyar APC.
Da ya ke bayyana sakamakon zaben a hedikwatar INEC da ke Kano a yau Lahadi, jami’in zaɓen, Farfesa Adamu Jibril ya bayyana Kwankwaso a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 25,072
Ya kuma sanar da Tinubu na APC da kuri’u 16,773, PDP 2,477, jam’iyyar Labour ta samu kuri’u 202.
CREDIT /Daily Nigerian Hausa via Facebook search.
0 Response to "DADUMINSA, Kwankwaso ya doke Tinubu a mahaifar Ganduje "
Post a Comment