DADUMINSA, Ajilesoro ya lashe kujerar majalisar wakilai ta Ife a PDP
Sunday, 26 February 2023
Comment
Ajilesoro ya lashe kujerar majalisar wakilai ta Ife a PDP
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana Taofeek Ajilesoro na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar tarayya ta Ife a ranar Asabar.
Jami’in zabe na INEC, Farfesa Abdulfatai Makinde ne ya bayyana Ajilesoro, wanda ya samu kuri’u 53,078 a matsayin wanda ya lashe zaben a babban dakin tattara sakamakon zaɓe na Ife a yau Lahadi a Ile-Ife.
Mista Makinde ya ce dan takarar jam’iyyar APC, Benjamin Adereti, ya samu kuri’u 51,051.
Ajilesoro dan majalisar wakilai ne, mai wakiltar mazabar tarayya ta Ife a majalisar wakilai.
SOURCE /CREDIT/Daily Nigerian Hausa via Facebook search.
0 Response to "DADUMINSA, Ajilesoro ya lashe kujerar majalisar wakilai ta Ife a PDP"
Post a Comment