Bola Tinubu Ya Lashé Zaɓèn Kananan Hukumomin 10 A Jíhar Ekiti
Bola Tinubu Ya Lashé Zaɓèn Kananan Hukumomin 10 A Jíhar Ekiti
Hukumar zabe ta kasa ta ayyana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zabe a kananan hukumo 10 a jihar Ekiti.
Baturen zaben INEC na jihar kuma shugaban jami'ar lafiya ta tarayya da ke Ila Orogun, jihar Osun, Farfesa Akeem Lasisi, shi ne ya bayyana sakamakon yankunan.
Ya ce Tinubu ya samu nasara da kuri'u mafiya rinjaye a waɗan nan kananan hukumomin yayin da Atiku Abubakar, na jam'iyyar PDP ke yake masa baya a matsayin na biyu.
Daily Trust ta ruwaito tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi ne ya zo na uku, sai kuma Rabi'u Musa Kwankwaso na NNPP a matsayin na hudu a jihar.
CREDIT /Dokin karfe TV via Facebook search.
0 Response to "Bola Tinubu Ya Lashé Zaɓèn Kananan Hukumomin 10 A Jíhar Ekiti "
Post a Comment