Wata jami'a a Nijeriya ta hana ɗalibai amfani da wayoyin zamani
Wata jami'a a Nijeriya ta hana ɗalibai amfani da wayoyin zamani
Jami’ar Bingham da ke Karu, a Jihar Nasarawa ta fitar da sanarwar hana dalibai amfani da wayoyin zamani
Sanarwar, mai ɗauke da kwanan wata, 18 ga Janairu ta sanar da ɗalibai cewa an ɗauki matakin ne biyo bayan karya dokokin makaranta game da amfani da wayar hannu na zamani.
Sanarwar ta kara da cewa, “Bayan karya dokoki akai-akai wajen amfani da wayoyin hannu, wanda ya saɓa wa sashe na 5.14 karamin sashe na I, II da III na littafin jagoranci ga dalibai, an haramta amfani da wayoyin komai-da+ruwanka da gaggawa.
"Za a kwace wayoyin waɗanda su ka karya wannan doka kuma za su fuskanci hukunci da ya dace."
Sanarwar ta ƙara da cewa bayan hana amfani da wayar hannu ta zamani, jami'ar ta ce dalibai na iya amfani da kwamfutocin su.
“Eh, mun hana amfani da wayoyin zamani kamar yadda aka bayyana a cikin bayanin magatakarda amma muna ba da izinin amfani da kwamfyutoci," in ji sanarwar.
SOURCE /CREDIT /Daily Nigerian Hausa via Facebook search.
0 Response to "Wata jami'a a Nijeriya ta hana ɗalibai amfani da wayoyin zamani"
Post a Comment