--
Ni zan kayar da Zulum a zaɓe mai zuwa, ƴar takarar gwamna a Borno ta ci alwashi

Ni zan kayar da Zulum a zaɓe mai zuwa, ƴar takarar gwamna a Borno ta ci alwashi

>

 








Ni zan kayar da Zulum a zaɓe mai zuwa, ƴar takarar gwamna a Borno ta ci alwashi


Yar takarar gwamna a jihar Borno a jam'iyyar ADC, Fatima Abubakar, ta ce tana da kwarin gwuiwar lashe zaben gwamnan na ranar 11 ga watan Maris, duba da ci gaban da aka samu a baya-bayan nan.


Abubakar, mace daya tilo da ta tsaya takara a zaben ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a Maiduguri ra yau Laraba cewa ta fara kamfen gida-gida don jin ta bakin al’ummar jihar.


Ta ce tana samun karin goyon baya da farin jini daga masu zabe, tana mai cewa ta kusa samun nasarar lashe zaben.


“Ina kara samun farin jini tare da karin magoya baya, musamman matan da suka yi imani da karfina na kawo sauyi mai inganci a rayuwar mata da matasa a Borno.


"Ina so in yi kira ga mata da matasa da muke tuntubar juna, suma su isar da sakon ga wasu kan bukatar a gwada 'yan mata 'yan takara a wannan takara don samun canji mai kyau," in ji Abubakar.


Credit /Daily Nigerian Hausa via Facebook search. 

0 Response to "Ni zan kayar da Zulum a zaɓe mai zuwa, ƴar takarar gwamna a Borno ta ci alwashi"

Post a Comment