Duk da matsin lamba suke fuskanta, CBN ya sha alwashin kawo karshen amfani da tsofaffin takardun naira a ranar 31 ga Janairu.
Duk da matsin lamba suke fuskanta, CBN ya sha alwashin kawo karshen amfani da tsofaffin takardun naira a ranar 31 ga Janairu.
A ranar Asabar ne kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta bi sahun masu kira da a tsawaita wa’adin amfani tsofaffin takardun naira.
A wata sanarwa da Malam Bello Galadanci, sakataren yada labarai na kungiyar ACF reshen jihar Kano ya fitar a ranar Asabar, kungiyar ta ce wa’adin ranar 31 ga watan Janairu da gwamnatin tarayya ta kayyade ya kusan dakile ayyukan tattalin arziki a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa kin karbar tsoffin takardun naira a hada-hadar kasuwanci saboda fargabar rashin iya saka kudaden a bankunan kasuwanci na janyo wa talakawa wahala.
An kuma yi irin wannan kiraye-kirayen a fadin kasar.
Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a yammacin ranar Asabar, CBN ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya kan wa'adin.
SOURCE, Rahama Tv via Facebook search.
0 Response to "Duk da matsin lamba suke fuskanta, CBN ya sha alwashin kawo karshen amfani da tsofaffin takardun naira a ranar 31 ga Janairu."
Post a Comment