--
Asibitin ATBUTH zai fara maganin larurar rashin haihuwa

Asibitin ATBUTH zai fara maganin larurar rashin haihuwa

>

 





Asibitin ATBUTH zai fara maganin larurar rashin haihuwa


Asibitin koyarwa na Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, ATBUTH, Bauchi ya sanar da cewa zai fara maganin larurar rashin haihuwa ga ma’auratan da ba su da haihuwa.


Babban Daraktan Asibitin, Dakta Yusuf Bara ne ya bayyana haka a wajen bikin kaddamar da manhajar bayanai ta na'ura mai ƙwaƙwalwa, a wani bangare na shirin kula da lafiya ta yanar gizo da aka yi a jiya Alhamis a Bauchi.


Ya ce ana horar da kwararrun likitocin babban asibitin a cibiyar lafiya ta NISA da ke Abuja domin saukaka gudanar da maganin cikin sauki.


“Likitocin mata, likitocin mahaifa da ma’aikatan jinya a halin yanzu suna samun horo a Asibitin Firimiya na NISA, Abuja.


"Bugu da ƙari, sanannen likitan mata a fannin rashin haihuwa da IVF, Dokta Ibrahim Wada zai kasance a matsayin mai sa idanu a fannin mata masu ciki da mata, don tabbatar da shirin cikin sauƙi da kuma ayyuka masu inganci," in ji shi.


A cewarsa, tawagar kwararru da masu bincike daga kungiyar likitocin ATBUTH/NISA da sauran abokan hulda za su fara gudanar da bincike na hadin gwiwa don samar da maganin cutar sikila

.

SOURCE, DAILY NIGERIAN HAUSA VIA FACEBOOK SEARCH 

0 Response to "Asibitin ATBUTH zai fara maganin larurar rashin haihuwa"

Post a Comment