Zaa fara koyarda yara da yaren uwa a najeriya.
Thursday, 1 December 2022
Comment
Image source /credit Nigeria reporters Hausa via Facebook
Zaa fara koyarda yara da yaren uwa a najeriya.
Maaikatar ilmi ta dakatar da koyarwa da yaren turanci a makarantun Firamaren Najeriya.
Wannan ya biyo bayan sabon tsarin da gwamnatin tarayya ta ƙirƙiro, wanda ya wajabta koyarwa da yaren uwa a matakin Firamare.
Hakan na nufin, a jihar Kano, da sauran jihohin da Hausa yafi tasiri, yaren zai zama hanyar koyar da darasi a makarantun.
Ministan ilimi, Adamu Adamu, yace daga matakin ƙaramar Sakandire, za'a riƙa haɗawa da turanci wajen bayar da darasin.
source /credit Nigeria reporters Hausa via Facebook
0 Response to "Zaa fara koyarda yara da yaren uwa a najeriya. "
Post a Comment