Yau Tanko Yakasai yacika shekara 97, anya kuwa akwai mai shekarun sa a yan siyasar kano.
Alhamdulilah ina yiwa Allah godiya da ya nuna mana ranar haihuwar mahaifin mu Alhaji Salihu Abubakar wanda aka fi sani da Tanko Yakasai OFR, wanda a yau yake cika shekaru 97 da haihuwa. Tabbas Allah Ya yi wa mahaifina baiwar yawan rai da koshin lafiya, ga zuri'a mai yawa da albarka. Alhamdulilah!
Su biyu iyayen sa suka haifa da yar'uwar sa, wadda ita kuma Allah baiwa tsahon rai ba, amma shi Allah Ya yara shi kuma ya bashi yara har 21 wanda kowannen mu yayi makarantar boko da ta Muhammadiya, kuma duk mun yi aure da iyalan mu Alhamdulilah.
Kamar yadda wasu suka san tarihin sa, shi bai je makarantar boko ba, da kansa ya koyi karatu kuma ya shiga makarantar manya inda ya koyi karatu da rubutu ya samu ilimin da ya samu wanda a yau har farfesoshi yana cin gyaran su Alhamdulilah. Sannan ya san ilimin addini sosai, har tafsirin Al’qur’ani Mai Girma ada yana yi a gida, kuma yayi karance karancen littattafan addinin musulunci daban daban wanda wasu ma ya haddace su. Alhamdulilah!
Sannan a bangaren gwagwarmaya kuwa kowa yasan irin sadaukar da rai da gudunmawar da ya bayar wajen kwatoya talaka yancin sa a jihar Kano da arewa da ma kasa baki daya, ya fara gwagwarmaya tun yana da kimanin shekaru 24 kuma har yanzu bai daina ba, kaga kenan ya sadaukar da shekaru 70 na rayuwar sa wajen hidimar al'umma. Kuma shine manyan yan NEPU na karshe da Allah Ya bar mana, duk sa'annin sa da su kayi NEPU tare da Mallam Aminu Kano Allah Yai musu rasuwa, sai dai na kasa kasa. Duk sa'annin sa da sukayi fafatukar tabbatar da siyasar damokuradiya a Arewa da ma kasar nan, kusan shi kadai Allah Ya bari a yanzu. Alhamdulilah!
Muna godewa Allah da Ya bar mana Baba, ya kawo wannan shekaru cikin lafiya da cikakkiyar nutsuwa, tunanin sa bai gushe ba, hankalin sa bai gushe ba, kusan duk tarihin abubuwan da suka faru a baya suna nan akan sa bai manta su ba, ya ga 'ya'ya da jikokin sa, har ma da tattaba kunne. Wannan ba karamin arziki bane. Alhamdulilah!
Muna kara godewa Allah bisa wannan ni'ima da yai wa mahaifinmu da mu kan mu, da ma al'umma baki daya. Muna rokon Allah Ubangiji Ya kara masa lafiya da yawan rai, domin mu ci gaba da kwankwadar shawarwari da ilimi daga gun sa, muna adduah Allah Ubangiji Yai masa jinkiri mai albarka, Ya Sa karshen sa yai kyau, Ya bamu ikon koyi da shi, da kare mutuncin sa da sunan sa, Ya kuma jikan mahaifan sa, sannan Ya sada mu a aljanna baki daya ranar gobe Qiyama, amin Ya Rahman. Alhamdulilah!
Salihu Tanko Yakasai
Dawisun Kanawa
Dan takarar Gwamna a Jam'iyar PRP
Masoyin Kano da Arewa da Najeriya.
Source /credit/Salihu Tanko Yakasai via Facebook.
0 Response to "Yau Tanko Yakasai yacika shekara 97, anya kuwa akwai mai shekarun sa a yan siyasar kano. "
Post a Comment