SABBIN KUƊI: Bankin CBN ya haramta liƙi a wurin biki, cumuimuye naira, rubutu a kai, kekketawa ko dangwala mata datti
IMAGE SOURCE /CREDIT /Premium Times Hausa via Facebook search.
SABBIN KUƊI: Bankin CBN ya haramta liƙi a wurin biki, cumuimuye naira, rubutu a kai, kekketawa ko dangwala mata datti
Ashafa MurnaibyAshafa Murnai December 14, 2022
SABBIN KUƊI: Bankin CBN ya haramta liƙi a wurin biki, cumuimuye naira, rubutu a kai, kekketawa ko dangwala mata datti
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tunatar da cewa har yanzu dokar haramta liƙi ko tattaka naira a wurin bukukuwa ta na nan daram.
CBN ya ce dokar ta tanadi ɗaurin wata shida ko kuma tarar naira 50,000 a kan duk wanda ya karya dokar.
Don haka ne Babban Bankin Najeriya ɗin ya ce duk wani nau’i, salo ko sigar lalata naira ba za a sake lamuncewa da shi ba, dokar hukuncin ɗauri ko tara za ta yi aikin ta kam duk wanda ya karya dokar.
Sashe na 21(3) na Dokar CBN ta 2007, ya tabbatar da tanadin irin hukuncin da za a yi wa wanda ya karya dokar.
Babbar Manajar Ayyukan CBN, Ngozi Etim ce ta yi wannan gargaɗin, lokacin da ta ke ganawa da manema labarai.
Ta ce CBN ya samu haɗin kai da hukumar ‘yan sanda, FIRS, EFCC da kuma NFIU domin magance matsalar yadda ake lalata takardun naira.
Ngozi ta yi tir da ɗabi’ar yin watsi da kuɗaɗe a wurin bukukuwa. Ta ce kamata ya yi idan mutum zai yi kyautar bajinta, to kamata ya yi wanda zai bayar da kyautar kuɗaɗen a cikin ambulan ya bayar.
“Bai kamata a riƙa cumuimuye kuɗaɗe ba, a riƙa saka su a cikin ambulan.
“Bai kamata ana ɓata naira da mai ba. Kada a bari mai ya riƙa taɓa naira. A riƙa ajiye kuɗi ana tsaftace su, kamar yadda mutum ke tsaftace suturar sa.
SOURCE /CREDIT /Premium Times Hausa via Facebook search.
0 Response to "SABBIN KUƊI: Bankin CBN ya haramta liƙi a wurin biki, cumuimuye naira, rubutu a kai, kekketawa ko dangwala mata datti"
Post a Comment