Rano Air ya ɗauki ɗaliban da Kwankwaso ya kai karatun tukin jirgin sama aiki
Rano Air ya ɗauki ɗaliban da Kwankwaso ya kai karatun tukin jirgin sama aiki
Sabon kamfanin jigilar jirgin sama, Rano Air, ya bada aiki ga wasu daga cikin daliban da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya kai kasar Jordan su ka karanci ilmin tukin jirgin sama.
Kamfanin, mallakar Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, shahararren mai kasuwancin mai ɗin nan na A.A Rano ya ɗauki daliban aiki ne su bakwai domin su zamo daga cikin matukan jiragen sa.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa matasan su bakwai, dukkansu ƴan asalin jihar Kano ne.
Matasan su ne kamar haka:
Capt. Abubakar bello danfulani
Capt. Bashir Danladi garba
Capt. Habibu yakubu bechi
Capt. Yunus Abba yunus
Capt. Abdulmajid said Sanjay
Capt. Idiris baba idi
Capt. Umar gwarzo
CREDIT /SOURCE /Daily Nigerian Hausa via Facebook search.
0 Response to "Rano Air ya ɗauki ɗaliban da Kwankwaso ya kai karatun tukin jirgin sama aiki"
Post a Comment