Majalisar Wakilan Najeriya ta umarci babban bankin Najeriya CBN da ya janye sabuwar dokar hada-hadar kuɗi:
Image source /Facebook
Da Ɗuminsa:
Majalisar Wakilan Najeriya ta umarci babban bankin Najeriya CBN da ya janye sabuwar dokar hada-hadar kuɗi:
Daga Sani Twoeffect Yawuri
Majalisar Wakilan ta umarci Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele da ya dakatar zartar da kudirin sabuwar dokar hada-hadar kuɗin da zata fara aiki a ranar 9/1/2023 har sai anbi umarnin kudirin dokar da ta kafa bankin.
Haka kuma Majalisar Wakilan ta umarci Gwamnan babban bankin da ya bayyana a gabanta domin yi mata cikakken bayani akan sabbin dokokin hada-hadar kuɗin da bankin keta fitowa dasu a ƴan kwanakin nan.
A zaman majalisar na yau Alhamis 8/12/2022 ƴan majalisar da dama sunyi Allah wadai da waɗannan sabbin dokokin inda sukace waɗannan dokokin zasu gurgunta tattalin arzikin ƙananan masana'antu musamman a yankunan karkara inda basu da bankuna a kusa dasu.
Daga karshe dai majalisar wakilan ta umurci Gwamnan babban bankin ya bayyana a gabanta ranar Alhamis 15/12/2022 domin gamsar da ita akan barin sababin dokokin suyi aiki
SOURCE /CREDIT /Rariya on Facebook
0 Response to "Majalisar Wakilan Najeriya ta umarci babban bankin Najeriya CBN da ya janye sabuwar dokar hada-hadar kuɗi:"
Post a Comment