--
Hanya mai sauki wajan gyaran Jiki lokacin sanyi

Hanya mai sauki wajan gyaran Jiki lokacin sanyi

>

 




GYARAN JIKI LOKACIN SANYI


Ina yawan samun tambayoyi masu alaka da gyaran fata a irin Wannan lokaci na sanyi kasancewar wadansu matan jikinsu yakan bushe fatar tayi tauri kuma namiji yana bukatar lallausan jiki idan kinga mijinki bayason hada jiki dake to ki bincika jikinki


Ki samu ayaba mai kyau ki bare ko ki matse da hannunki ko ki markada yayi laushi sai ki zuba madara peak ki fasa kwai amma farin zaki zuba banda jan ki matsa lemon tsami ki gauraya sosai sai ki shafa a jikinki yayi sa a daya (1hour) sai kiyi wanka da ruwan zafi amma ba zafi sosaiba Idan kinayin wannan har kwana uku zakiga yanda jikinki zaiyi


sannan zaki iya daka ganyen magarya ki zuba cikin man zaitun ki hada da man habbatussauda sai ki dinda shafawa ajikinki bayan sa a daya (1hour) sai kiyi wanka fatarki zatayi laushi


haka kuma sabulun salo shima ana hadashi da ganyen magarya a kwabashi da man habbatussauda dan kadan bayan ya hade ya zama sabulu saiki rinka wanka dashi shima yana gyara fata sosai jikinki yayi laushi.


Source /credit /sirrin rike miji on Facebook. 

0 Response to "Hanya mai sauki wajan gyaran Jiki lokacin sanyi "

Post a Comment