--
Gwamna Matawalle ya bada umarnin a kawar da jiga-jigan jam'iyyar mu a Zamfara -- PDP

Gwamna Matawalle ya bada umarnin a kawar da jiga-jigan jam'iyyar mu a Zamfara -- PDP

>

 





Gwamna Matawalle ya bada umarnin a kawar da jiga-jigan jam'iyyar mu a Zamfara -- PDP


Jam’iyyar PDP ta zargi gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, da kafa wani gungun ƴan daba, tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro domin kawar da jiga-jigan jam’iyyar adawa a jihar, a daidai lokacin da ‘yan sanda su ka janye tsaron ɗan takarar gwamna na PDP a jihar, Dauda Lawal.


Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa ‘yan sanda sun fara wani mumunan samame da nufin kamawa tare da tsare wasu manyan shugabannin jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, tare da yi musu ƙage.


Da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya ce Jam’iyyar APC ta dimauce saboda karuwar farin jinin PDP da ‘yan takararta gabanin babban zabe na 2023.


“Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke cike da rudani sakamakon ƙaruwar farin jinin jam’iyyar PDP da ‘yan takararmu gabanin zabukan 2023, ta kara zage dantse wajen murkushe ‘yan takarar PDP da sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa a kokarinta na rufe bakin shugabannin PDP da dakatar da su sabo da karbuwar da jam'iyyar mu ta yi a kullum ga 'yan Najeriya.


“Yayin da mu ke yi muku jawabi a yau, an ruwaito cewa gwamnatin APC, karkashin Gwamna Bello Matawalle a Jihar Zamfara ta kafa wata rundunar kashe-kashe tare da hadin gwiwar wasu ‘yan sanda, wadanda suka fara murkushewa, kamawa, da tsare wasu fitattun shugabannin PDP a Jihar Zamfara bisa zarge-zargen da ba su da tushe a cikin shirin APC na musgunawa shugabanninmu da sauran masu ra’ayin rikau a jihar.


“PDP na da labarin yadda aka yi wa dan takarar PDP na Sanata kuma Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben gwamna a jihar Zamfara, Ikra Aliyu Bilbis, Captain Bala Mai Riga, da wasu fitattun ‘ya’yan jam’iyyar PDP, aka kama, aka tsare su ba bisa ka’ida ba da ƴan sanda su ka yi bisa umarnin Gwamna Matawalle.


“An kuma sanar da jam’iyyar mu game da shirin gwamnatin APC karkashin jagorancin Gwamna Matawalle na kamawa tare da tsare dan takarar gwamnan PDP a jihar Zamfara, Dakta Dauda Lawal,” inji shi.


Don haka PDP ta bukaci “Sufeto Janar na ‘yan sanda da ya gaggauta maido da da tsaron da aka janye wa dan takarar Gwamnan Jihar Zamfara a jam’iyyar PDP tare da daukar matakan gaggawa don tabbatar da samar da isasshen tsaro ga ‘ya’yan PDP a jihar bisa aikin da tsarin mulki ya ba shi.


SOURCE /CREDIT /Daily Nigerian Hausa via Facebook. 

0 Response to "Gwamna Matawalle ya bada umarnin a kawar da jiga-jigan jam'iyyar mu a Zamfara -- PDP"

Post a Comment