EFCC Na Neman AA Zaura Kan Zargin Damfara
Monday, 5 December 2022
Comment
EFCC Na Neman AA Zaura Kan Zargin Damfara
Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki EFCC ta ce tana neman dan takarar Sanata na Jam’iyyar APC a Jihar Kano Abdulkareem Abdulsalam Zaura, wanda aka fi sani da AA Zaura.
Hukumar na neman dan siyasar ne domin gurfanar da shi a kotu kan zargin damfara ta Dala miliyan 1.3.
EFCC na so ta sake gabatar da shi ne gaban kotun daukaka kara wadda ta soke hukuncin baya da ya wanke AA Zaura daga zargin.
Source/credit/Rahama Tv via Facebook
0 Response to " EFCC Na Neman AA Zaura Kan Zargin Damfara"
Post a Comment