Dalibai za su fara zanga-zanga bisa tsare Aminu Mohammed wanda ya yi suka ga Aisha Buhari
Dalibai za su fara zanga-zanga bisa tsare Aminu Mohammed wanda ya yi suka ga Aisha Buhari
Kungiyar dalibai ta kasa, NANS, ta ce za ta fara wata zanga-zangar ta ba ƙaƙƙauta wa a fadin kasa, domin neman a sako wani dalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutse a Jihar Jigawa, Aminu Mohammed, wanda aka kama aka kuma kai shi gidan yari a kan wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter yana sukar matar shugaban ƙasa, Aisha Buhari.
A wata sanarwa da shugaban NANS, Usman Barambu, ya sanyawa hannu a jiya Alhamis, kungiyar ta bayyana cewa za a fara zanga-zangar ne a ranar Litinin mai zuwa har sai Mohammed ya samu ƴancinsa.
DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa tun da farko kungiyar dalibin ta nemi afuwar uwargidan shugaban kasar kan abin kunyar da Mohammed ya wallafa a shafinsa na twitter da ya janyo mata da iyalanta, yayin da ta kuma bukaci a sako dalibin.
Sai dai kungiyar ta bayyana cewa ta gaji da bi ta lallami kan a saki Mohammed, inda ta ƙuduri aniyar yin zanga-zanga.
“Mun yi tuntuba da kuma bi ta lallami wanda bai samar da wani sakamako mai kyau ba wajen neman ƴancin Mohammed, don haka za a fara zanga-zangar kamar haka: Litinin, 5 ga Disamba, 2022 a duk fadin kasar nan.
"Sabo da haka a sani cewa zanga-zangarmu za ta ci gaba har sai an sake shi ba tare da wani sharadi ba," in ji sanarwar.
Source /credit /Daily Nigerian Hausa via Facebook
0 Response to "Dalibai za su fara zanga-zanga bisa tsare Aminu Mohammed wanda ya yi suka ga Aisha Buhari"
Post a Comment