Boxing Day" - rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti - ta samo asali ne a lokacin mulkin Sarauniyar Ingila Victoria a shekarun 1800.
Image source /credit /Facebook search
Boxing Day" - rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti - ta samo asali ne a lokacin mulkin Sarauniyar Ingila Victoria a shekarun 1800.
Ranar ba ta da wata alaƙa da wasan damben boxing da ake gudanarwa a faɗin duniya.
Sunan ya samo asali ne sakamakon ƙunshe kyauta da masu arziki ke yi a cikin akwati kafin su bai wa mabuƙata - 'box' na nufin akwati a harshen Hausa.
Boxing Day a al'adance, ita ce ranar da bayi kan yi hutun aiki sannan su karɓi kyautuka na musamman daga iyayen gidansu.
Haka nan, a ranar ce su ma suke zuwa gida domin bai wa iyalansu akwatunan kyautar.
Tarihin gicciye Yesu a mahangar addinin Kirista
A yankunan Catalonia na Spain da Ireland na Birtaniya, suna yin bikin ranar ne da sunan "Saint Stephen's Day".
A ƙasashen Turai kuma kamar Hungary da Jamus da Poland da Netherlands, suna kallon Boxing Day a matsayin Ranar Kirsimeti ta biyu
Tara kuɗi
Su ma coci-coci sun taka rawa wurin ƙirƙirar Boxing Day. Sukan karɓi kuɗi daga masu bauta a tsawon shekara baki ɗaya domin bai wa mabuƙata a lokutan Kirsimeti.
Sukan ajiye kuɗin a cikin akwatuna kafin a buɗe su a Ranar Kirsimeti, sai kuma a bai wa mabuƙata kwana ɗaya bayan Kirsimeti wato Boxing Day.
Sai dai a yanzu ba a fiya amfani da akwatunan ba kamar da.
Yaushe ne Boxing Day?
Boxing Day, ita ce rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti, wadda ke faɗowa ranar 26 ga kowane Disamba.
Kuma rana ce ta hutu a Najeriya da wasu ƙasashen duniya.
Idan ta faɗo ranar Asabar, akan mayar da hutunta zuwa Litinin ta gaba.
Idan kuma ta faɗo ranar Lahadi, to ranar Talata ne hutun.
Credit / BBC Hausa via Facebook.
0 Response to "Boxing Day" - rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti - ta samo asali ne a lokacin mulkin Sarauniyar Ingila Victoria a shekarun 1800."
Post a Comment