--
Babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad

Babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad

>

 








IMAGES SOURCE/CREDIT /BBC Hausa via Facebook search. 


Babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad.


An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same shi da dukkan laifi huɗu da ake tuhumar sa da su.


Daga cikin tuhumar da ake yi masa akwai da zargin tayar da tarzoma a jihar Kano ta hanyar wa'azinsa.


Bayan an same shi da laifukan, sai Mai Shari'a Sarki Yola ya ɗage zaman kotun don ba shi damar rubuta hukuncin da za a yanke wa malamin.

Bayan dan lokaci kuma sai aka koma zaman kotun tare da yanke hukuncin.


Sai dai kafin a tafi hutun, Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara ya yi magana ta karshe inda ya ce bai san lauyan da ke kare shi ba kuma ba ya neman afuwa saboda, a cewarsa, bai aikata laifi ba kuma ya nemi a gaggauta yanke masa hukunci.


Mai Shari'a Sarki Yola ya ce malamin yana da kwana 30 don ɗaukaka ƙara idan bai gamsu da hukuncin ba.


A ranar Juma'a 16 ga watan Yulin 2021 ne gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama'a, zargin da ya sha musantawa.

Cikin iƙirarin da Abduljabbar ya yi a wa'azizzikan da ya sha gabatarwa, wadda kuma ake tuhumar sa a kanta, har da maganar cewa Annabi Muhammadu ya yi ƙwacen mata mai suna Safiyya daga wani sahabinsa.


Mai Shari'a Ibrahim Sarki Yola ya ce malamin "ya gaza kare wannan da'awa ko iƙirari da ya yi da karɓaɓɓun hujjoji".


Ɗaya daga cikin lauyoyin gwamnatin Kano, Farfesa Mamman Lawan Yusufari, ya faɗa wa BBC Hausa cewa sun gabatar da shaidu huɗu don tabbatar da laifin da suke zargin malamin da shi.

Ƙari a kan hukuncin kisa da kotun ta yanke, ta kuma ba da umarnin ƙwace dukkan litattafan da Sheikh Abduljabbar ya gabatar don kare kan sa da su.


An bayyana litattafan da suka kai kusan 200, waɗanda shehin malamin ya yi amfani da su yayin zaman muƙabalar da aka gudanar a watan Yulin 2021 da zimmar kare da'awarsa.


Kotun ta ba da umarnin a miƙa litattafan ga Babban Ɗakin Karatu na Jihar Kano.


Bugu da ƙari, kotu ta haramta saka karatun malamin a dukkan kafofin yaɗa labarai na jihar, tare da bai wa gwamnati shawarar ta ɗauki "duk matakin da ya dace" kan wadda ta saɓa umarnin.


Haka nan, ta ba da umarnin rufe masallatan Abduljabbar biyu.


BBC ta yi yunƙurin jin ta bakin lauyan malamin amma ba mu samu damar yin hakan ba.

SOURCE /CREDIT /BBC Hausa via Facebook. 

0 Response to "Babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad"

Post a Comment