Ana rade radin DR Aminu yunusa dangwani zai dawo Kwankwasiyya
DA DUMI DUMINSA: rikicin jam iyyar PDP a Jihar Kano ana rade raden Dakta Adamu yunusa dangwani zai dawo tafiyar kwankwasiyya bayan sabani da aka samu tsakaninsa da uban gidansa sanata rabi'u Musa kwankwaso.
Idan baku mantaba a baya Adamu yunusa dangwani ya raba gari kwankwaso ne sabida takarar gwamna da Dr dangwani yakeso a Bashi shiyasa yaki bin kwankwaso Sabuwar jam iyyar NNPP ya cigaba da Zama a jam iyyar PDP sabida Yana ganin zai samu abinda yake bukata wato takarar gwamna.
Dangwani yayi wasu maganganu kan jagoran kwankwasiyya kan cewa jam iyyar PDP Babu abinda batayi musu ba, itace Rufin asirin kwankwaso sabida haka Babu abinda zai sa yabar jam iyyar PDP ya koma wata jam iyya harma yake ikirarin sune suka taimaki kwankwaso da Yan kwankwasiyya
Amma Yanzu watakila dangwani zaiyi mi'ara koma baya ya dawo wajan tsohon uban gidansa sanata rabi'u Musa kwankwaso ko me yayi zafi?
Source/credit /Trust News Hausa TV 📺 via Facebook.
0 Response to "Ana rade radin DR Aminu yunusa dangwani zai dawo Kwankwasiyya "
Post a Comment