Aisha Buhari ta janye karar da ta kai Aminu Muhammad, lawyansa C.K. Agu ya shaida wa BBC
Friday, 2 December 2022
Comment
Cikin wani saƙon tes, Barista C.K. Agu bai yi ƙarin bayani ba game da dalilin da ya sa Aisha ta janye ƙarar.
Matakin na zuwa ne bayan ɗalibin, wanda ke karatu a Jami'ar Tarayya da ke Dutse, ya shafe kwana uku a gidan yari da ke Suleja bisa umarnin kotun.
A ranar Litinin ake sa ran ci gaba da zaman kotun don sauraron neman beli da lauyan Aminu ya yi a zaman ranar Talata da aka yi, wanda bai yi nasara ba.
Matar shugaban na zargin Aminu da ɓata mata suna saboda saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter maƙale da hotonta tare da cewa "ta ci kuɗin talakawa".
Ƙungiyoyin kare haƙƙi da masu sharhi sun soki Aisha game da matakin da ta ɗauka bayan rahotanni sun yi zargin cewa sai da aka lakaɗa wa Aminu duka kafin gurfanar da shi a gaban kotun.
Kazalika, wasu sun soki matashin kan zargin da ya yi wa matar shugaban.
SOURCE /CREDIT /BBC Hausa via Facebook.
0 Response to "Aisha Buhari ta janye karar da ta kai Aminu Muhammad, lawyansa C.K. Agu ya shaida wa BBC "
Post a Comment