--
ABIN A YABA: Wata Kirista Ta Baiwa Musulmai Gudummawar Siminti Buhu Hudu Domin Gina Masallaci

ABIN A YABA: Wata Kirista Ta Baiwa Musulmai Gudummawar Siminti Buhu Hudu Domin Gina Masallaci

>

Images Source /credit/Rariya via Facebook. 

ABIN A YABA: Wata Kirista Ta Baiwa Musulmai Gudummawar Siminti Buhu Hudu Domin Gina Masallaci 

Wata Kirista a garin Mararraba dake karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa ta bada gudummawar siminti buhu hudu don gudanar da ginin wani masallacin Juma'a da aka rushe domin sabunta shi. 

Masallacin wanda ake yi wa lakabi da Masallacin Sani Zamfara (Zamfara Mosque) dake unguwar Tudun Wada a garin na Mararraba, dandazon al'ummar musulmai dake yankin ne suke fito a safiyar yau Asabar domin yin aikin gayya don ganin an soma dora tubalin gininsa.

Matar dai wadda kabilar Yarbawa ce, ta yi matukar shan yabo a wurin musulman unguwar bisa gudummawar bazatan da ta yi musu duba da cewa ba addininsu daya ba.

SOURCE /CREDIT /Rariya on Facebook 

0 Response to "ABIN A YABA: Wata Kirista Ta Baiwa Musulmai Gudummawar Siminti Buhu Hudu Domin Gina Masallaci "

Post a Comment