Yar uwata da zaki daina bleaching (shafe shafe) da kin Rabu da wadannan Matsalolin
Image Source /credit /Facebook.
KI DAINA BLEACHING.
-
"Babu wata riba ko abin burgewa a cikin yin bleaching, domin haƙiƙa yin hakan saɓawa Allah ne, canza halittar Allah ne. Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yace Allah ta'ala ya tsinewa masu canza halittar Allah ko waɗanda ake canzawa ɗin"
-
"Abin ban haushi da takaici, da yawan ƴan mata da samarin mu sun mayar da ɗabi'ar yin bleaching tamkar wata gasa abar so a addini, sun ɗauke sai sunyi bleaching ɗin ne za su auru ko kuma su sami ababen so a rayuwarsu, wanda kuma hakan haƙiƙa saɓawa Allah ne"
-
"ki daina bleaching, ki daina bleaching haka Allah yakeso ya ganki baƙa, ba wai bazai iya yin farar bane, ai yayi fararen da yawa, to haka yake so ya yiki kuma yayi ki. Kiyi godiya ma Allah ba abinda za ki rasa a rayuwa. ba wani abu a duniya da fara ta samu baƙa ta rasa wannan abun."
Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
-
Muhammad Umar Baballe.
Abu Amatillah.
Source /credit /sirrin rike miji on Facebook.
0 Response to "Yar uwata da zaki daina bleaching (shafe shafe) da kin Rabu da wadannan Matsalolin "
Post a Comment