--
Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam.

Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam.

>

 





 Image Source : Facebook 

An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a garin Daura, a shekara ta 1962

(ko da yake wani lokacin Yakan CE 1964).


Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, a Mijin Wurin Yayarsa,Mallam

Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza,

kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa Kano.


Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, Wanda

asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano. Tun kafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978.


Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. 


Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen

kasar Misra a cibiyar yada Al ' Adun Rude Misra, Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta

Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru

na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. 

Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu: Waccan makarantar ya je ta da Daddare Bayan Sallar Lsha ' in, waccan kuma ta koyo harshen

larabcin da yamma. 


Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983.

Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. 


A shekara ta 1989,ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta

Ilimin Tafsi wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. 


Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar

Kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Kasa-Da-Kasa Ta Afrika da take Khartoum, Sudan.


Sannan kuma, kafin Rasuwarsa,ya yi kokari wajen kammala karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir (Phd), a Jami ' ar usman dan Fodiyo da take Sokoto.


Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar,

Sheikh Abdul-Aziz Ali al- Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar dandago,wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu

Littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab a wajensa. 


Akwai kuma Jibrin Abubakar Sheikh Limamin Masallacin Juma ' at BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano. 


Daga cikin malamansa na jami'a

kuma, akwai Sheikh Abdurrafi ' u da Dr.. Khalid

Assabt.


Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar da su, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai Girma, kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, ARB'UNA

Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam,

Riyaadussalihiin, SiiratunNabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus salaatun nabiiy.


Wasu daga cikin daliban malam sun hada da Malam Rabi ' u umar r / lemo da

Malam Sani Abdullahi Alhamidi dorayi da Mallam Abdullah Usman da Malam Usman Sani Haruna da Malam Ibrahim Abdullahi Sani Da Malam Yunus Ali Muhammad da Dr.. Salisu Shehu da Malam Shehu Hamisu Kura da malam anas Muhammad Madabo.


Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wannan cibiya (Sheikh Ja ' afar Islamic Documentation Centre).


Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428

(13/04/2007) sakamakon harin da wadansu 'yan ta'adda suka kai masa, a daidai lokacin da

Yake jagorantar sallar asuba a Masallacin Jumaa na dorayi.


Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa.


Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka Halarci Jana ' Izarsa, kuma

an binne shi ne a makabartar Dorayi. 


Allah ya ji kan sa ya Gafarta Masa, yayi masa tagomashi da gidan aljanna. 

Amin

SOURCE :umar idris bin jauro Facebook 


0 Response to "Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam."

Post a Comment