Shugaba Buhari ya amince da yi wa ma'aikatan shari'a ƙarin albashi
Friday 18 November 2022
Comment
Shugaba Buhari ya amince da yi wa ma'aikatan shari'a ƙarin albashi
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shirin ƙara wa ma’aikatan shari’a na ƙasar albashi.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yau Juma’a a jihar Rivers, lokacin ƙaddamar da sabon ginin makarantar horas da lauyoyi da ke jihar.
Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami, wanda shi ne ya wakilci shugaban ƙasar, ya ce gwamnatin ƙasar tana ƙoƙarin inganta albashin ma’aikatan shari’ar ne domin ƙarfafa ɓangaren da kuma tabbatar da ƴancinsa.
Ya ce yanzu haka shugaba Buhari ya umurci shugaban hukumar tarawa da raba kuɗaɗen haraji na ƙasar, da ministan sharia’a su ɗauki matakan ganin an fara aiwatar da ƙarin albashin
Source 👉.Mikiya Hausa Labarai 24 on Facebook.
0 Response to "Shugaba Buhari ya amince da yi wa ma'aikatan shari'a ƙarin albashi"
Post a Comment