--
Mun ƙwato Naira biliyan 117 a wata 8 - ICPC

Mun ƙwato Naira biliyan 117 a wata 8 - ICPC

>

 






Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya bayyana cewa hukumar ta kwato sama da Naira biliyan 117 tsakanin watan Janairu zuwa Agusta.


Owasanoye ya bayyana hakan ne a gaban kwamitocin majalisar wakilai kan yaki da cin hanci da rashawa a lokacin da hukumar ke kare kudurin kasafin kudin 2023 a Abuja.


Kakakin hukumar, Azuka Ogugua ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis.


Ta ce yayin da ya ke magana kan kasafin kudin shekarar 2022, shugaban ya bayar da takaitaccen bayanin kudaden da aka kwato da su ka hada da biliyan N1.413 da dala $225,965 a asusun ajiyar ICPC/TSA da tsabar kudi har biliyan N1.264bn ta hanyar haraji.


Sauran abubuwan da aka kwato sun hada da filaye, gine-gine da aka kammala, motoci, na’urorin lantarki da gwala-gwalai, wadanda kudinsu ya kai miliyan 679.13m, N2.603bn, N81.1m, N1.55m da N195,500.


Baya ga kwato kudaden, shugaban ya kuma bayyana wasu nasarorin da hukumar ta samu a lokacin tsarin kasafin kudin shekarar 2022 wanda ya hada da kammala bincike 672 da kuma bincike 565 da ba a kai ga korafe korafe ba.

Source 👇


DAILY nigerian Hausa on Facebook. 

0 Response to "Mun ƙwato Naira biliyan 117 a wata 8 - ICPC"

Post a Comment