--
 kwarewa a fagen girki daya ne daga cikin muhimman abubuwa da suke fito  da martabar ’ya mace,

kwarewa a fagen girki daya ne daga cikin muhimman abubuwa da suke fito da martabar ’ya mace,

>

 



Image source 👉Facebook. 


kwarewa a fagen girki daya ne daga cikin muhimman abubuwa da suke kara fito da daraja da martabar ’ya mace, ko a gidan mijinta take ko a gidan iyayenta.


Domin mace a gida ko da ba ta da aure, matukar ta iya girki kada ka so ka ga yadda ake haba-haba da ita. Za a ga yadda kodayaushe mutanen gidan ke yi mata fatan samun miji nagari domin ana da yakini mijin da za ta aura zai more wa mace, ba don komai ba sai don iya girkinta.


Har ila yau, a bangaren matar aure wajibi ne ta iya girki iri-iri domin da iya girki ne kadai za ta iya mallakar zuciyar mijinta cikin ruwan sanyi. Wani muhimmin abu da ya kamata ki yi la’akari da shi shi ne: tsabta, kafin ki fara dafa abincin ya kasance duk kayayyakin da za ki yi amfani da su, ki wanke su ki rufe su a gyare, kuma yana da kyau ki tara hankilinki wuri guda, don gudun kada ki manta da wani abu, domin da kin manta da wani abu to lissafi ya kwace shi ke nan sai girki ya ki dadi. Haka nan kada ki ce wai sai kin gama girki sannan za ki yi wanke-wanken kwanuka ko cokula. A’a yi kokari ki yi kafin ki sauke abinci.

Hakazalika, idan har ba ki iya girki ba, to yi kokari ki lallabi kawarki ko wata da kika san ta iya ta koya miki.


Yana da kyau ki fahimci cewa koyon girki a zamanin nan ba shi da wuya, domin za ki iya koya a kafafen watsa labarai kamar jaridu da mujallu da gidajen rediyo da talabijin da kuma littattafan Hausa.


Har ila yau, kina iya koya a shafukan sada zumunta kamar su: Facebook da WhatsApp da Twitter da sauransu.


Marigayi Dokta Mamman Shata Katsina yana cewa: “Kada fa mu bar abincinmu na gargajiya,” wannan batu haka yake, babu shakka abincinmu na gargajiya ba abin yadawa ba ne, misali mu dauki tubani kin iya girka shi kuwa? Yanzu idan aka matsa ba ki iya mandako ba fa? To biski fa?


 Haka nan akwai abinci na gargajiya irin su dambu da biski da dan wake da dan bagalaje da kwado da gudan kurna, matan zamani yanzu sai ka ga wai abin kunya tuwo ba ta iya ba, wannan abin kunya ne a gare ki.


Hakika yawancin maza suna bukatar abincin gargajiya, amma in da gizo ke sakar shi ne matansu ba su iya ba, babu yadda za su yi, sai dai idan suna so su je gidajen abinci su sayo abin da suke marmari, ko su yi hakuri, amma matukar suka samu wacce ta kware kada ka so ka ji yadda take shan yabo daga gare su.


Babu shakka iya girki ga mace babbar hanya ce ta fita kunyar mai gida da ’yan uwa, sannan cikakkiyar dama ce da mace za ta iya amfani da ita wajen mallake miji cikin sauki, shi kuwa zuwa wajen bokaye don mallake miji babu abin da yake haifarwa sai da-na-sani da nadama.

Source 👇


Sirrin rike miji on Facebook. 

0 Response to " kwarewa a fagen girki daya ne daga cikin muhimman abubuwa da suke fito da martabar ’ya mace, "

Post a Comment