KUNGIYAR MASU SAI DA MAGUN GUNA TACE MASU CHEMIST SUGUJI SAI DA MUGGAN KWAYOYI GA MATASA.
Kungiyar masu sana’ar sayar da magunguna a kyamist ta yi kira ga masu sana'ar kan su guji sayar da magungunan da ke sa maye ko sayar da maganin ba bisa ka’ida ba musanman ga matasa.
Shugaban kungiyar na kasa reshen jihar Kano Muhammad Nura Abubakar ne ya yi kiran ta cikin shirin Zaman Yan Murina inda ya mayar da hankali kan hayoyin da za’a bi wajen magance ta’ammali da gurbatattun magunguna a cikin al’umma.
Muhammad Nura ya ce kungiyar bata goyon bayan sayar da magunguna masu sa maye
Shugaban kungiyar masu sayar da magungunan a Kyamis yace babbar matsalar da take damun masu sana’ar itace rashin hukumar da zata dinga kula da masu sayar da maganin a matakin kasa da kuma jiha.
Muhammad Nura ya yi kira ga 'yan majalisun tarayya da sanatocin jihar kano kan su kai kudirin gaggawa akan hakan duba da muhimmancin da sana’ar take dashi wajen taimakawa marasa lafiya.
A karshe ya bukaci masu sana’ar kan su dinga neman ilimi akan samin magunguna tare da bincike akai
SOURCE : Rahama Tv on Facebook.
0 Response to "KUNGIYAR MASU SAI DA MAGUN GUNA TACE MASU CHEMIST SUGUJI SAI DA MUGGAN KWAYOYI GA MATASA. "
Post a Comment