--
KOTU TA HANA KWACE KADARORIN TSOHUWAR MINISTAR MAN PETIR DA KE LONDON

KOTU TA HANA KWACE KADARORIN TSOHUWAR MINISTAR MAN PETIR DA KE LONDON

>

 





Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Maitama babban birnin tarayya Abuja ta hana Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa EFCC karbe wasu kadarori hudu a Landan da ke da alaka da tsohuwar Ministar Man Fetur, Misis Diezani Allison-Madueke bisa kuskure.


Kotun, a wani hukunci da mai shari’a Olukayode Adeniyi ya yanke, ta kuma haramtawa babban mai shigar da kara na tarayya, da hukumar kare laifuffuka ta kasa birtaniya da kuma wasu masu binciken Burtaniya uku- Helen Hughes, da Stacey Boniface da kuma John Bavister- daga kwace kadarorin.


Mai shari’a Adeniyi ya bayyana cewa, shaidun da ke gaban kotun sun tabbatar da cewa kadarorin da aka ambata mallakar wani hamshakin attajiri ne, Mista Benedict Peters da kamfanoninsa.


SOURCE : RAHAMA TV FACEBOOK. 

0 Response to "KOTU TA HANA KWACE KADARORIN TSOHUWAR MINISTAR MAN PETIR DA KE LONDON "

Post a Comment