--
Kidayar 2023: Hukumar ƙidaya za ta ɗauki ma'aikatan wucin-gadi miliyan 2, in ji Kwamishina

Kidayar 2023: Hukumar ƙidaya za ta ɗauki ma'aikatan wucin-gadi miliyan 2, in ji Kwamishina

>

 





Kidayar 2023: Hukumar ƙidaya za ta ɗauki ma'aikatan wucin-gadi miliyan 2, in ji Kwamishina


Ayodeji Ajayi, kwamishinan tarayya mai wakiltar Ekiti a Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa, NPC, ya bayyana cewa za a ɗauki ma'aikatan wucin-gadi miliyan 2 da za su yi aikin ƙidaya.


Ajayi ya bayyana hakan a Ado Ekiti a yau Alhamis a wani taron manema labarai don sanar da jama'a game da shirin daukar ma'aikatan wucin-gadi domin yin aikin.


Ajayi ya yi gargadin cewa duk wani ma’aikaci da aka dauka a ka dame shi da aikata rashin gaskiya kafin, lokacin da kuma bayan aikin to za a hukunta shi tare da wanda ya tsaya masa.


Domin tabbatar da daukar mata da yawa a aikin, hukumar NPC ta bayyana cewa a jihar Ekiti za ta dauki mafi karancin kashi 40 cikin 100 na mata a matsayin ma’aikatan wucin gadi domin gudanar da aikin.


Mista Ajayi, wanda tsohon shugaban ma’aikatan jihar Ekiti ne, ya ce: “Hukumar za ta dauki ma’aikatan wucin gadi a har mutane miliyan biyu a fadin kasar nan domin gudanar da wannan atisayen, wannan ya hada da ma’aikatan NPC da ma’aikatan wucin gadi da za a horas da su da sauran kwararru.


"Kuma duk wani matashi mai neman aikin yi, wanda ya shiga aikin kuma ya yi aiki mai kyau, hukumar za ta ba shi satifiket domin inganta aikinsa."


Ya bayyana cewa, hukumar na yiwa galibin ma’aikata a ma’aikatan jiha da tarayya, da kuma ‘yan Najeriya masu sha’awar aiki, tare da tabbatar da gaskiya a matsayin ma’aikata, inda ya bukaci masu sha’awar su nuna sha'awar shiga aikin ta adireshin yanar-gizo: censusadhocrecruitment.nationalpopulation.gov.ng.


SOURCE : DAILY NIGERIAN HAUSA FACEBOOK 

0 Response to "Kidayar 2023: Hukumar ƙidaya za ta ɗauki ma'aikatan wucin-gadi miliyan 2, in ji Kwamishina"

Post a Comment