--
KALLI MAKUDAN KUDADEN DA AMURKA TA WARE WAJAN SAIDO AKAN ZABEN NIGERIA NA 2023

KALLI MAKUDAN KUDADEN DA AMURKA TA WARE WAJAN SAIDO AKAN ZABEN NIGERIA NA 2023

>

 




Kasar Amurka ta ware dala miliyan 50 domin kula da yadda za'a gudanar da babban zaben kasar nan na shekarar 2023.

Kasafin kudin zai kunshi horar da 'yan jarida, da kungiyoyin fararen hula da taimakon fasaha da sauransu don tabbatar da zabe na gaskiya.


Babban Jakadan Amurka, Mista Will Stevens ne ya sanar da hakan a yau Litinin a Ibadan babban birnin jihar Oyo yayin wani taron bude taron karawa juna sani game da zaben wanda aka shirya wa 'yan jarida da Cibiyar Yada Labarai ta Afrika ta Yamma ta shirya.


Will ya lura cewa gwamnatin Amurka tana aiki kafada da kafada da abokan huldarta karkashin Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) don tabbatar da cewa kowace kuri’a tana da kima.


Ya jaddada cewa Amurka za ta ci gaba da jaddada darajar kada kuri'a da kuma kare 'yancin 'yan jarida masu sanya idanu kan harkokin zabe.


SOURCE: Rahama Tv on Facebook. 

0 Response to "KALLI MAKUDAN KUDADEN DA AMURKA TA WARE WAJAN SAIDO AKAN ZABEN NIGERIA NA 2023 "

Post a Comment