--
Idan a ka cire tallafin man fetur sai ya koma lita ɗaya N410 -- NNPC

Idan a ka cire tallafin man fetur sai ya koma lita ɗaya N410 -- NNPC

>

 



Shugaban kamfanin man fetur ta NNPC a Najeriya, Mele Kyari ya ce farashin litar mai zai kai N410 kan kowanne lita guda, maimakon N170 da ake sayarwa a yanzu, da zaran an janye tallafin mai.


Kalaman Mele Kyari na zuwa ne kwana guda bayan kungiyar dillalan mai ta kasa na cewa su na son a kai farashin man naira 200 zuwa 210 domin saukaka wahalhalun mai a faɗin kasar.


IPMAN ta ce janye tallafi ko karin kuɗin mai ne kawai mafita a wannan yanayi da Najeriya ke ciki.


Sai dai a lokacin da ya ke jawabi a gaban 'yan majalisar wakilai, shugaban NNPC ya ce ana cikin wani yanayi saboda a halin yanzu cigaba da sayar da man kan naira 170 abu ne mai wahala, saboda farashin ya ninka haka sau uku.


Don haka dole ne wani ya rinka daukan asara, kuma yanayi ne da ba zai ɗore ba.


Kusan tun a farkon wannan shekara zuwa wannan lokaci ba a daukar wani dogon lokaci ba tare da an faɗa cikin karancin fetur ba a Najeriya.


Wannan ne ya sa farashin ya sauya a cikin watanni baya, abin da ya kawo sauki a wancan lokaci. Sai dai makonni bayan hakan sai wahalar ta sake kunno kai kuma har yanzu ana cikinta.



SOURCE :  DAILY NIGERIAN HAUSA FACEBOOK 

0 Response to "Idan a ka cire tallafin man fetur sai ya koma lita ɗaya N410 -- NNPC"

Post a Comment